Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Biraye Suna Dauke Da Fiye Da Miyagun Cututtuka 60


Biri
Biri

Biraye na dauke da fiye da kwayoyin cututtuka iri 60 masu hadari ga mutane, Uade Ugbomoiko, masanin dabbobi a Jami’ar Ilorin ya fadi haka ranar laraba.

Biraye na dauke da fiye da kwayoyin cututtuka iri 60 masu hadari ga mutane, Uade Ugbomoiko, masanin dabbobi a Jami’ar Ilorin ya fadi haka ranar laraba.

Yayinda yake Magana a Ilori, Mr. Ugbomoiko yace wani kwaro da ake kira "Mastdomys natalensis" shine wurin da kwayar cutar zazzabi na lassa ke zama, cutar da kwanannan ta kashe rayuka da yawa a kauyen Ekpoma da kewayen ta cikin jihar Edo.

Yace binciken da aka gudanar a wadansu kauyukan jihar Edo ya gano kala kalan kwayoyin cuta guda takwas daga beraye iri daban daban. Yace yayanin rueran sama yakan shafi kasancewar kwayoyin da kuma berayen.

Ya gargadi ‘yan Najeriya su tsabtace gidajen su da kewayensu kowanne lokaci domin korar beraye, ya kara da cewa wasu manyan beraye sun fi yawa a gidaje da wuraren da mutane ke zama da rani.

Ya baiyyana cewa saboda kona daji da kuma neman abinci, beraye suna cika gidaje da rani kana su koma daji a lokacin ruwan sama.

Masanin ya gano wasu dalilai na yanayi kamarsu talauci, rashin ilimi, rashin tsabtar wuraren zama, da sauran wasu dalilan da ka iya kawo yaduwar wadannan kwayoyin cutar.

Ya kuma ce, “Kyautata lafiyar ‘yan Najeriya daga matsalar kwayoyin cuta na iya samuwa ne tawurin biyan bukatun mutane daga gwamnati.”

Melinda Gates

BIDIYO: COVID-19 VOA Ta Yi Hira Da Melinda Gates Kan Dalilin Da Yasa Suke Taimakawa Afirka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:08 0:00
Karin bayani akan Bidiyo
XS
SM
MD
LG