Wasu masu kutsen satar bayanan na’urar Kwamfuta sun saki dinbin bayanan sirri ta yanar gizo, wanda ke nuna cewa sun yi kutse a cikin kundin bayanan ‘yan kasar Turkiyya fiye da Miliyan 50. Bayanan da suka hada da bayanan mutum da iyalansa.
Wanda ya hada da lambar zaman dan kasa, adireshi da ranakun haihuwa da sunan iyayen mutum. Cikin wadanda suka ce an sami bayanan rayuwarsu har da na Shugaban kasar Recep Tayyip Erdogan da Firaminista Ahmet Davutoglu.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press, sun yi wani gwajin jeka-na-yika da wasu bayanan mutane guda 10 da basu zama daga wadanda aka sace ba, inda suka hada da wasu bayanan na barayin bayanan, wanda kuma akalla bayanai 8 daga cikin 10n sun yi daidai dana kundin bayanan da aka saki din.
Sakon da masu satar bayanan suka bada ta yanar gizon shine na yin tambaya, “Shin wannan koma-bayan kimiyya da fasahar, ko mukamai ba tare da tantance asali ba, ko kuma tsatstsauran ra’ayin addini zai iya zama durkushewar Turkiyya da ita kanta wannan kimiyyar mai rauni?”