Yau babbar rana ce ga Yarima Harry da Meghan Markle, yayin da masoyan biyu ke shirye-shiryen aurensu a garin Windsor da ke wajen birnin London a yau Asabar.
Yarima Harry shi ne na shida a jerin masu jiran gadon masarautar Ingila.
A farkon makon nan ne, Markle, wacce tsohuwar jaruma ce a fagen fitowa a fina-finai, ta bayyana cewa mahaifinta ba zai halarci daurin auren ba, saboda rashin Lafiya da yake fama da ita.
Rahotanni sun ce an yi wa, Thomas Markle, wanda ke zaune a Mexico, tiyata a ranar Larabar da ta gabata, sanadiyar wata cuta da yake fama da ita a zuciyarsa.
Ana sa ran za a ga dandazon jama’a da masu fatan alheri, wadanda za su halarci bikin auren da zimmar za su ga ma’auratan a zahiri.
Dubban ‘yan sanda aka jibge a garin na Windsor, a wani mataki da aka jima ba a ga irinsa ba a ‘yan shekarun nan, wanda za a biya da kudaden jama’a, abinda wasu suka yi ta suka akai.
Akalla baki 600 aka gayyata, mafi aksarinsu wadanda suke da alaka ta kut-da-kut da masu auren.
Batutuwan Da Za Su Fi Jan Hankali a Auren Yarima Harry Da Meghan
- Kayan da amarya Meghan za ta saka.
- Telan zamanin da ya dinka kayan amarya Meghan.
- Meghan za ta zama amarya ta farko da ba za ta samu rakiyar mahaifinta ba a wajen auren a tarihin masarautar - saboda ba shi da lafiya.
- Amma duk da haka sunan Thomas Markle na ci gaba da kasancewa a jerin sunayen baki.
- Wannan ne karon farko da za a samu amarya a masarautar mai gamin launin fata - wato mahaifin Meghan bature ne mahaifiyarta kuma bakar fata ce.
- Masu sharhi na hasashen cewa auren Yarima Harry zai dishar da tauraruwa ko kuma farin jinin Yarima William da uwargidansa Kate.
Facebook Forum