A wani taro da manema labarai daraktan labarai na sojojin Najeriya Manjo Janar John Eneche yace rundunar sojojin na muba'aya ga shugabancin kasar kuma tana bayan wannan gwamnati daram dam.
Injjishi zasu cigaba da yiwa tsarin mulkin kasar biyayya ba tare da yin wata wata ba. Yace duk wani fargaban juyin mulki a kawar dashi domin ba manufarsu ba ce.Yace sojojin Najeriya masu biyayya ne ga tsarin dimukradiya.
Akan zawarcin da aka ce 'yan siyasa na yiwa wasu sojoji Manjo Janar Eneche yace suna daukan matakai. Yanzu suna bukatar lokaci domin gudanar da bincike.
Shi ma kakakin sojojin Birgediya Janar Kukasheka yace sojojin Najeriya gaba daya sun ta'allaka ne kan biyayya ga shugaba Muhammad Buhari da kuma tsarin mulkin kasa. Yace duk yadda za'a yi, zasu yi iyakacin kokarinsu su kare gwamnatin da tsarin mulkin kasar.
Ga rahoton Hassan Maina Kaina da karin bayani.
Facebook Forum