A jihar zamfara dubun dubatan magoya bayan Janar Buhari, dan takarar shugabancin Najeriya karkakshin jam'iyyar APC, sunyi zaman jira sama'a da sa'o'oi 14 daga safiya har karfe 10 na dare, lokacinda janar Buhari ya isa birnin Gusau.
Wannan jiran bai sa magoya bayan sun nuna gajiya ba. Wasu suka gayawa wakilin Sashen Hausa Murtala Farouk Sanyinna cewa idan da ta kai su jira har zuwa jumma'a, zasu yi haka saboda su dai ga Janar Buhari, da nuna goyon bayansu.
A jawabinsa ga magoya bayansa a jihohin Zamfara da Kebbi, Janar Buhari yayi akkawarin inganta harkokin noma domin samar da ayyukan yi ga matasa. Haka kuma ya bayyana takaicin cewa sojojin Najeriya har ta kai suna gayawa kafofin yada labarai na kasashen waje irinsu su Sashen Hausa na Muriyar Amurka cewa ana tura su fagen yaki ba tareda wadatattun nkayan yaki ba. Yaci gwamnatinsa zata yi maganin wannan matsala da duka sauran matsalolin tsaro.
Wasu magoya bayan Janar Buhari sun taka da kafa na kilomita 36 domin su ga Janar Buhari.
Ga rahoto