Hukumar Zaben Najeriya, INEC, ta ce ita kam a shirye take domin gudanar da babban zaben watan Fabrairu mai zuwa, abinda ya saba da kalamun da aka ji daga bakin mai ba shugaban Najeriya shawara kan tsaro, Kanar Sambo Dasuki mai ritaya, wanda ya nemi a jinkirta zaben saboda rashin kammala raba katunan jefa kuri'a na dindindin.
Shugaban hukumar ta INEC, Farfesa Attahiru Jega, yace su kam, a shirye suke su gudanar da zabe a ko ina a cikin Najeriya.
Yace duk wani mai neman a dage zabe, to saboda wasu dalilansa ne amma ba dalilan da suka shafi hukumar zabe ko ayyukan da take yi ba.
Shi ma kakakin hukumar, Nick Dazan, ya bayyana cewa tun bayan wancan zabe na shekarar 2011 suka fara shirin wannan, kuma a inda ake yanzu, babu abinda ba su tsara na gudanar da wannan zaben ba.
Yace batun katunan jefa kuri'ar na dindindin ma ana samun nasara sosai wajen raba sauran da suka rage.