Kakakin hukumar kawar da bala’in ya fada a yau Litinin cewar mutane sun nemi matsugunai a kowane lungun tsibirin wasu kuma sun ketara zuwa makwabciyar tsibirin ta Lombok.
Mutane da suka arce daga gidajensu sun ninka fiye da sau hudu tun daga ranar Juma’a, yayin da tsananin motsin aman wuta ke kara ta’azzara, kuma yana haifar da tsoro aukuwar aman wuta daga tsaunin Dutsen Agung a karon farko cikin sama da sama da shekaru hamsin da ganin irin haka.
Dutsen dana wani yanki, kimanin kilomita 75 daga wani wurin masu yawon bude ido, ya fara nuna alam tun ciki watan Agusta.
An samu jerin aman wutar dutse a tsaunin Agung tsakanin shekarun 1963 zuwa 1964 kuma ya kashe mutane 1,100 kana ya jikata wasu daruruwa.
Facebook Forum