Barayin shanu sun kai hari a wasu kauyuka uku dake karamar hukumar Tsafe dake jihar Zamfara inda suka kasha mutane 26 tare da sace shanu da kayan abinci.
A cewar wani mazaunin yankin, wanda bai so a ambaci sunansa ba, ya shaidawa Muryar Amurka cewa, maharan sun soma kai hari ne tun a ranar Lahadi a kauyuka uku; Gangare, Gangama da kuma unguwar Dauda, duk a cikin karamar hukumar Tsafe.
Yayinda barayin suka saci shanu a Gangare, da aka bisu aka kwato shanun har aka yiwa wani daga cikinsu duka. Ba da dadewa ba barayin suka koma kauyen suka fara da kashe mutum na farko da suka tarar bakin shiga kauyen. Mutanen kauyen sun sake bin barayin amma basu sani ba cewa barayin sun gayyato wasu barayin su taimake su. Barayin dai sun shiga kauyukan ne kan Babura suna kashe- kashe.
A cewar wani da aka yi abun kan idonsa, barayin sun kashe na kashewa, suka kone shaguna da gidaje, sannan suka tasa shanu gaba suka wuce dasu.
Yayinda Muryar Amurka ta tuntubi kakakin ‘yan sanda na jihar yace shi ma a lokacin ne ya fara samun labarin abun da ya faru. Mutanen kauyukan sun nemi taimakon ‘yan sanda amma basu ga kowa ba sai wajen goma na daren Lahadi lokacin da suke kokarin binne wadanda suka rasa rayukansu. Akwai ma inda ‘yan sandan basu kai ba sai safiyar Litinin inda kuma jim kadan suka yi tafiyarsu.
A cewar wani barayin suna samun mafaka ne a wani gari kusa dasu. Ya ce sun sansu, sun san iyayensu, sun san gidansu, “amma babu yadda mutum zai yi magana sai su kasheshi da bindiga”
Yanzu dai mutanen kauyukan uku sun kaura daga gidajensu.
A saurari rahoton Murtala Faruk Sanyinna
Facebook Forum