Matasan masu zanga zangar sun fito ne dauke da alluna da kwalaye masu sakonnin nuna gajiyawa da kai hare-hare, da kisan kiyashi, da yawaitar satar mutane domin karbar kudin fansa, da ya-ki-ci ya-ki-cinyewa a jihar Zamfara.
Baya ga zagayawa a manyan titunan birnin Gusau, 'yan zanga-zangar sun yada zango a Majalisar dokokin jihar inda suka gabatar da koken nasu.
Daya daga cikin jagororin wannan zanga-zangar ta lumana, Dakta Sulaiman Shu'aibu Shinkafi jami'i na kungiyar kare hakkin bil adama ta Amnesty International a Jihar Zamfara ya bayyana cewa, sun fito ne domin su nuna wa duniya cewa, kashe-kashen da ake yi ya yi yawa don haka ya kamata gwamnati ta dauki mataki, in kuma ba za ta iya ba, ta sauka ta ba wa wadanda za su iya daukan kwakkwaran mataki.
Kungiyar ta kuma yi kira ga shugaban kasa, inda suka ce, tura ta kai bango, ana kashe 'yan uwansu, ba su da ikon zuwa gona ga yanayin damuna ya zo kuma suna cikin fargaba.
Sun kuma yi kira ga gwamnatin tarayya ta kafa dokar ta baci a Zamfara Jihar da ta fi ko ina yawaitar kisan kai a kasar.
Ya kara da cewa, an san inda barayiun suke amman anki ayi maganin su.
Kwamishinan watsa labarai na jihar, Sanda Muhammad Danjari, ya ce, wannan ba shi ne mafita ga matsalar tsaron da ke addabar jihar ba, yace abin da ya kamata su yi wa Zamfara shi ne su wuce Abuja su yi zanga-zangar domin ba gwamna ke da sojoji da yan sandan da za su magance matsalar ba.
Ya kuma yi kira ga masu kishin Zamfara da su ci gaba da zanga-zanga har gwamnatin tarayya ta dau mataki.
Facebook Forum