Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Bankin Musulunci Na Duniya Zai Hada Gwiwa Da Gwamnatin Jihohi Don Taimakawa Al'umma


Bankin Musulunci Na Duniya
Bankin Musulunci Na Duniya

Yayin da wasu jihohi a Najeriya musamman na arewa ke fuskantar kalubale a bangarori daba daban, hukumomi na duniya na ci gaba da kai dauki domin taimakawa jihohin a sassa daban daban na rayuwa.

Abinda ke nuna haka shi ne wata ziyarar gani da ido da Bankin Musulunci na duniya ya kai a wasu jihohin arewa don yin hadaka da gwamnatoci don kyautata rayukan jama'ar su, duk da yake masu ruwa da tsaki na korafi akan irin wannan hadakar.

Tun daga lokacin da Najeriya ta zamo kasa 'yantacciya zuwa yau, gwamnatoci sun yi fadi-tashi wajen bunkasa fannonin daban daban kamar Ilimi, lafiya, noma da sauransu, amma har yanzu kwalliya ta kasa biyan kudin sabulu a wadannan fannonin.

Wannan baya rasa nasaba da yadda har yanzu hukumomi da kungiyoyi na kasashen duniya ke shigowa musamman a arewacin kasar domin bayar da na su gudumawa don a samu ci gaba a fannonin da suke bayar da tallafin.

Wannan karon, Bankin Musulunci ne na Duniya ya shigo jihohin arewa a wani bangare na shirin tsara ayukan da zai bayar da tallafi akan su a shekara ta 2024 mai kamawa.

A wata ziyara a Sakkwato dake arewa maso yammacin Najeriya jagoran ayarin na bankin musulunci Mr. Jeff Khan yace sun ziyarci jihohin Katsina, Yobe da Sakkwato a kan wannan shirin na bayar da tallafi.

A jihar Sakkwato bankin zai bayar da tallafi ne a bangarorin lafiya da ayukkan noma, kuma ya zo ne domin haduwa da gwamnati su tattauna yadda shirin zai gudana yadda za'a ci moriyar sa.

Sai dai jagoran ayarin ya koka a kan ganin sau da yawa ake gudanar da shiraruwa daga baya a bari su lalace.

Masu ruwa da tsaki a harkar noma, daya daga cikin bangarorin da bankin zai yi aiki, sun bayyana cewa matsalar da bankin ke fargabar samu, abu ne da ake iya kaucewa idan gwamnati ta yi da gaske.

Masu lura da lamurran yau da kullum ma na da ganin cewa idan gwamnatocin sun shirya jama'arsu su amfana to zasu amfana, kamar yadda Farfesa Bello Bada na Jami'ar Usmanu Danfodiyo ta Sakkwato ke cewa.

Gwaman Sakkwato Ahamd Aliyu Sokoto yace gwamnatin sa kam shirye take jama'arta su amfana da ayukkan na tallafin da bankin zai bayar.

Abin jira a gani shi ne yadda jama'ar zasu amfana, idan aka samu nasarar aiwatar da shirin bankin musuluncin ko akasin haka.

Saurari rahoton:

please wait

No media source currently available

0:00 0:03:29 0:00

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG