Kwamitin yakin neman zaben tsohon mataimakin shugaban Amurka, Joe Biden, na goyon bayan bukatar “a gaggauta yin sauye-sauye” a fannin rundunar ‘yan sandan Amurka, ba wai a rage kudaden da ake kashewa fannin ba.
Biden, wanda zai kara da shugaban kasa Donald Trump a zaben watan Nuwamba mai zuwa, “bai yadda da cewa a rage kudaden da ake kashewa ‘yan sanda ba in ji mai magana da yawun kwamitin Andrew Bates cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Litinin.
Sai dai Biden ya ce ya fahimci irin “takaici da fushin” da masu kiran a yi sauye-sauye ke ciki.
Wasu masu fafutukar kare hakin dan adam sun yi kira da a rage kudaden da ake kashewa ma’aikatun ‘yan sanda bayan mutuwar George Floyd – bakar fatar da ya mutu makonnin biyu a lokacin da ‘yan sanda ke rike da shi.
Facebook Forum