Bayanai sun nuna cewa an samu asarar rayuka lokacin da dubban mutane suka afkawa runbun adana abinci na gwamnatin jihar Kogi. Shedun gani da ido sun bayyana yadda cunkoson mutane cikin runbun ya haddasa tsananin zafi da ya yi sanadiyar mutuwar mutum uku.
Kwamishinan labarai na jihar Kogi, Mista Kensly Pamwo ya ce abin takaici ne yadda aka lalata kaddarori na miliyoyin Naira daga wasu zauna gari banza da aka dauki nauyinsu.
A jihar Neja, ranar Talata an fasa rumbunan ajiyar wasu yan kasuwa ciki har da na kamfanin Dangote dake garin Suleja, kamar Yadda shugaban hukumar bada agajin gaggawa na Jihar Neja, Alhaji Ibrahim ya tabbatar.
Masu sharhi dai sun ce jama’a sun fara wuce gona da iri dan haka akwai bukatar daukar mataki kamar yadda daya daga cikinsu malam Yusuf Ladan ya bayyanawa Muryar Amurka.
A halin da ake ciki dai, rundunar yan sandan jihar Neja ta ce ta kama wasu matasa 17 da suka shirya gudanar da wata zanga-zanga ba tare da izinin gwamnati ba.
Domin karin bayani saurari rahotan Mustapha Nasiru Batsari.
Facebook Forum