Za a gudanar da taron ne a tsakiyar watan gobe a Abuja, da hadin gwiwar Majalisar Musulunci da Duniya Rabita'atul alam islam, taron zai sami manyan malamai daga Saudiya da sauran sassan duniya.
Shiek Abdullahi Bala Lau, yace kokarin da gwamnatin Najeriya keyi ta yi dai dai, hakan ne yasa suka bi kasashen Afirka wanda suka hada kasar Benin da Nijar da Togo da Burkina Faso da Ghana don kira ga musulmai da su zo wannan taro don su bada kasidodi, su kuma nuna matsayin musulunci don gane da ta’addanci da sauran abinda akeyi da rigar musulunci.
Shima shugaban babban kwamitin shirya taron Dakta Bashir Isiyaku, yayi dirar mikiya kan tura yara su zama almajirai da sunan koyon karatun Alkur’ani, inda yace iyaye na da laifi don su suka haifi ‘ya ‘yan su da kuma tura su garuruwa masu nisa, batare da sanin inda ‘ya ‘yan su ke kwana ba ko abinda suke ci ko lafiyar su, hakan shike saka yaro ya tashi bashi da Imani da daukar munanan akidu.
Alkaluma daga cibiyar kididdiga ta Najeriya sun nuna akwai Almajirai dake gararanba kan tituna su miliyan 12 a Najeriya. kungiyoyin Ahlus sunnah sun dage wajen tsame akidarsu ta Salafanci daga cudanya da ta’addanci, don yadda ‘yan ta’adda ke fakewa da sunan Sunnah suna kashe mutane babu dalili.
Domin karin bayani.