'Yan kasuwan suna kokawa saboda kawo yanzu babu wani tallafi da suka samu daga gwamnatin jiha ko ta tarayya duk da alkawuran da gwamnatocin suka dauka can baya.
Yayinda suke jawabi a wajen taron rabon tallafi da wani dan majalisa ya bada, shugabannin 'yan kasuwan sun koka da rashin cika alkawuran da aka yi masu. Yanzu wasunsu sun koma maula domin ciyar da iyalansu.
Alhaji Ali Kachalla shugaban 'yan kasuwar Yola yace har yanzu basu bar mika kokon baransu ba. Sai ya kira gwamna da kakakin majalisar dokokin hijar cewa sun mika kokon baransu garesu.
Shi ma a jawabinsa shugaban kungiyar 'yan kasuwan Najeriya da mataimakinsa mai kula da jihohin arewa Alhaji Muhammad Ibrahim Etisi ya wakilta ya bukaci gwamnatocin arewa da su taimakawa 'yan kasuwa musamman a lokacin da suka fada cikin wani bala'i kamar ta gobara.
Shi ma dan majalisa da ya taimaka masu Onarebul Lawal Garba ya bukaci gwamnatoci da manyan kamfanoni su tallafa.
Ga karin bayani.