Wannan ziyara za ta kasance ita ce ta biyu bayan wacce ya kai a lokacin da kasar ta samun ‘yan cin kanta daga Sudan a shekarar 2011.
Ziyarar ta Ban, na zuwa ne a daidai lokacin da shirin aiwatar da matsayar samar da zaman lafiya da aka cimma a watan Agustan bara, tsakanin shugaba Salvar Kiir da tsohon mataimakinsa Riek Machar, ke tafiyar hawainiya.
Rahotanni sun ruwaito Machar yana ikrarin cewa ba zai je Juba domin kafa gwamnatin hadin kai ba, har sai dakarunsa dubu uku sun shiga birnin, da kuma karin wasu a 1,200 a garuruwan Bor da Malakal da Bentiu.
Ministan yada labaran kasar, Michael Makuei, ya ce za su yiwa Ban Ki-moon karin bayanin kan irin kokarin da su ke yi wajen ganin an aiwatar da yarjejeniyar.
Ya kara da cewa za kuma su yi mai bayani kan irin rawar da dakarun wanzar da zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya ke takawa a kasar ta Sudan ta Kudu.