MDD ta bude sabon helkwatarta data kafa domin yaki da cutar Ebola a Ghana. Ta girke tawagar da zata tsara matakan da hukumomin kasa da kasa zasu dauka domin yaki da cutar.
Jiya litinin ce shugaban tawagar Anthony Banbury, da ma’aikatansa suka isa Accra babban birnin kasar Ghana.
Wannan shine karo na farko da MDD zata kafa ofishin matakan gaggawa gameda batun kiwon lafiya.
Babban magatakardan MDD Ban ki-moon yace ofishin zai taimaka wajen hada kan matakan da hukumomin kasa da kasa suke dauka na tunkarar annobar Ebola, da tallafawa kasashen da cutar tafi yiwa jama’arsu illa d a suka hada a Laberiya da saliyo d a kuma Guinea.