Mazauna jihohin dake kudancin nan Amurka su na kokarin farfadowa daga bala’in ruwan sama da guguwa mai murdawa da suka kashe mutane kusan 330, wanda wannan shi ne bala’i irinsa mafi muni da aka gani cikin shekaru 80.
Jiya jumma’a, mutane da dama sun koma domin neman abinda ya rage daga cikin gidajensu da guguwa ta tafi da su, kwana biyu a bayan da daruruwan irin wannan guguwa suka yi kaca-kaca da wannan yanki.
Sai dai kuma, hanyoyin da ba su iya biyuwa, da rashin man fetur da wutar lantarki, su na kawo cikas ga kokarin kwashe tarkacen da ya bazu ko ta ina. Wani kamfanin bayarda shawara akan harkokin inshora yace irin hasarar da wannan bala’I ya janyo zai iya kaiwa dala miliyan dubu 5.
Shugaba Barack Obama na Amurka ya ganewa idanunsa wannan mummunar barnar jiya jumma’a a Jihar Alabama, a inda jami’ai suka tabbatar da mutuwar mutane 228, adadin da ya zarce na dukkan sauran jihohin da wannan hadarin ruwan sama da guguwa suka ratsa.
Shugaba Obama ya yi ma wadanda suka kubuta da rayukansu jaje, ya kuma fada musu cewa babban aikin da yasa a gabansa yanzu shi ne na taimaka musu domin su sake farfadowa. Yace irin hasarar dukiyar da aka yi ta shige misali, amma kuma irin juriyar da mutanen yankin suka nuna ya burge shi.
Mutane kimanin miliyan daya ba su da wutar lantarki yanzu haka a Jihar ta Alabama.
A bayan Jihar Alabama, mutane fiye da 30 sun mutu a jihohin Tennessee da Mississippi, yayin da mutane goma sha bibbiyu suka mutu a jihohin Georgia da Arkansas. Har ila yau, an samu hasarar rayuka a jihohin Virginia da Louisiana da kuma Kentucky.