Da yake nuna rashin jin dadinsa dangane da yadda gwamnatocin jihohi a Najeriya ke yiwa kananan hukumomi kama karya, shuagaban kungiyar NLC, Kwamarad Ayuba Wabba, ya ce ba zasu amince da hakan ba.
Ganin yadda gwamnoni ke takurawa kananan hukumomi har ta kai ga wasu lokuta ba a gudanar da zabe sai dai a nada Kantomomi, kuma kudade basa zuwa kai tsaye da kananan hukumomi, hakan yasa basa iya yin aikin komai. A cewar Kwamarad Ayuba.
A cewar wani tsohon shugaban karamar hukuma Kwamrad Aminu Abdussalam Gwarzo, na cewa an sami matsala ne tun farko bisa yadda ‘yan Majalisun jihohi suka zama tamkar ‘yan amshin Shata a hannun gwamnatocin jihohinsu.
Kananan hukumomi dai na da matukar muhimmanci ganin cewa sune matakin farko da ‘yan kasa zasu iya kai kukansu.
A baya-bayan nan ne kwamitin da gwamnatin APC ta kafa kan gyaran tsarin mulkin Najeriya, karkashin jagorancin gwamnan jihar Kaduna Nasiru El-Rufa’i ya bada shawarar a soke tsarin kananan hukumomi gaba daya.
Domin karin bayani saurari rahotan Hasssan Maina Kaina.
Facebook Forum