Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Buhari Ya Gayyaci Shugaban ‘Yansanda Saboda Rashin Zama Binuwai (Benue)


Wasu 'yansandan Najeriya wajen tabbatar da tsaro
Wasu 'yansandan Najeriya wajen tabbatar da tsaro

Batun tabbatar da tsaro a Najeriya ya dau wani sabon salo bayan da Shugaban Najeriya ya gayyaci Sufeto-Janar na 'yansandan kasar don bayyana dalilinsa na kasa cigaba da zama a Binuwai kamar yadda aka umurce shi.

Shugaba Muhammadu Buhari, wanda ya bayyana mamakin yadda aka yi Sufeto-Janar na ‘Yansandan Najeriya, Ibrahim Kpotun Idris, ya kasa zama a yankin Binuwai da Filato da Nasarawa har zai tashe-tashen hankali sun lafa kamar yadda ya ba shi umurni, ya gayyaci Sufeto-Janar din zuwa Fadarsa don jin dalili.

Wannan ya kuma biyo bayan korafe-korafen da al’ummar jahar ta Binuwai su ka yi game da hakan lokacin da Shugaba Buhari ya kai ziyara. Da alamar dai shi Sufeton ‘Yansandan ya na hutu ne na tsawon mako biyu lokacin da Buhari ya kai ziyara a jahar ta Binuwai.

A halin da ake ciki kuma ana ta bayyana muhimmancin daukar duk wani matakin da zai kawo karshen wannan kashe-kashen da ake yi a sassan Najeriya. Alal misali, tsohon Shugaban Kungiyar Kwadago ta Najeriya Suleiman Dan Zaki ya ce ya kamata a bai wa shugaban kasa cikakken hadin kai wajen wannan aiki na tsaro a fadin kasar saboda muhimmancinsa.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG