A ranar Juma’a katamfaren kamfanin yin magani na Pfizer ya sanar cewa ba zai nemi amincewar hukuma na gaggawa ba domin fito da rigakafin coronavirus a karshen watan Nuwamba.
Wasu kamfanoni biyu dake kokarin fito da maganin kuma sun dakata. Babu alamar kamfani na hudu zai fitar da sakamako sai karshen shekara.
Trump dai ya sha fadin cewa za a samar da maganin ga mutae da dama kafin ranar zabe, a wani kokari da gwamnatinsa ta yiwa lakabi, “Kammala Aikin Da Gaggawa” da ta kirkiro domin samar da maganin cikin gaggawa. Da dadewa masana kimiya na ciki da wajen gwamnatinsa suka ce ba zai yiwu a cimma wannan burin ba.
Da yake nuna alamar haka farkon watan nan, Trump ya dora laifi ga siyasa ba tare da bayani ba.
“Ina gani ya kamata mu samu kafin lokacin zabe,” Inji Trump a wani faifan bidiyo a shafinsa na tiwita bayan da aka sallame shi daga asibiti inda ya yi jinyar COVID-19.
A wani jawabi ranar Juma’a, shugaban Pfizer, Alber Bourla yace ya yiwu zuwa kashen Oktoba Kamfanin ya iya sanin ko rigakafin na aiki. Amma ba zai iya cimma ingancinsa ba har sai kusan karshen Nuwamba.
Boula ya wallafa cewa,“Aminci shi zai kasance burinmu na farko,”
Facebook Forum