Shafukan sada zumunta na social media na taka muhimmiyar rawa wajen samun labarai ko aika wa da sako a tsakanin al’umma.
Kafofi irinsu Facebook, Twitter, Badoo, Instagram, Google Plus,Whatsapp kan samar da labarai tare da sada zumunta cikin sauki.
Sai dai yayin da a kasashen da aka ci gaba akan yi amfani da wadannan kafofi ta hanyoyin da suka dace, a kasashe masu tasowa da alamun ba haka labarin yake ba.
Arch. Sa’adatu Aminu Raji, malama a babbar kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Adamawa, wato Adamawa state Polytechnic, ta ce, wasu har yanzu ba su iya amfani da wadannan kafofi ta yadda ya kamata ba.
A cewarta maimakon samun ilimi, labari ko fasaha, wasu sun koma yada karya da ta da husuma.
Shi ko Malam Muhammad Lawal Danladi, ya ce abun mamaki wasu sun yi amfani da hotunansu lokacin da aka samu tashin bam, wanda ya rutsa da su a massalacin kwalejin, wajen nuna hotunansu a matsayin daya daga cikin hotunan rikicin yankin Mambilla a jihar Taraba.
A cewar Malam Dandali, wannan abun ya ba shi mamaki.
Saurari rahoton Ibrahim Abdulaziz domin karin bayani:
Facebook Forum