Atoni janar na Amurka, Jeff Sessions, ya fadawa majalisar dokoki jiya asabar cewa zai bayar da shaida a gaban Kwamitin Kula da Ayyukan Leken Asiri na majalisar dattijai wanda yake binciken katsalandar da Rasha ta yi a zaben shugaban kasa na bara a nan Amurka.
Sessions yace yana son bayyana gaban Kwamitin domin amsa tambayoyin da suka kunno kai game da shi a cikin shaidar da tsohon darektan hukumar binciken manyan laifuffuka ta tarayya ta Amurka, James Comey, ya bayar a makon da ya shige.
Atoni janar din yace zai bayar da shaida gaban kwamitin jibi talata, watakila bayan yayi rantsuwa. Bai bayyana yadda zai gabatar da wannan shaida ba, ya Allah a bainar jama’a ko a cikin sirri.
Ma’aikatar shari’a, wadda take karkashin jagorancin Sessions, tana binciken hulda da tuntubar juna a tsakanin gwamnatin kasar Rasha da kwamitin yakin neman zaben shugaba Donald Trump kafin zaben watan Nuwambar bara, a lokacin ba a zabi Trump ba.
Facebook Forum