Alkalan da aka gurfanar sun hada da Justice Hyeladzira Nganjiwa da Muhammad Yunusa Nasir ana zarginsu da cin amanar ofishinsu da halarta kudaden haram bayan sun karba ta hanyar da bata dace ba.
Yayinda ake tuhumar Justice Muhammad Yunusa Nasir akan laifuka hudu shi ko Justice Nganjiwa yana fuskantar tuhuma ta laifuka 14 ne.
Hukumar EFCC ta bayyana tana da shaidu 33 da zata gabatar akan alkalan biyu.
Wai laifukan Justice Muhammad Yunusa sun hada da karban kudi har Naira miliyan daya da rabi daga hannun wani sanannen lauya Riki Tarfa. Shi ko Justice Nganjiwa ana zarginsa ne da karban wasu makudan kudi har dalar Amurka $144.000.00 da nufin yin zagon kasa ga wata shari'a dake gabansa.
Tuni 'yan Najeriya suka fara tofa albarkacin bakinsu akan wannan dambarwar kan matsayin EFCC da matsayin Majalisar Alkalai ta kasa.
Alhaji Musa Jika na wata kungiya mai fafutikar kare hakkin bil Adama yace yakamata shugabannin Najeriya su fahimci cewa maganar shari'a ana yinta ne bisa doka ba abun da shugaban kasa yake so ba. Yace yawancin shari'un da gwamnatin tarayya ke gabatarwa bata cika cin nasara ba saboda rashin kwararan hujjoji da rashin nagartattun lauyoyi.
A wani bangaren wani lauya mai zaman kansa Barrister Sheriff Ahmed Muhammad ya bayyana cewa matakin da Majalisar Alkalai ta kasa ta dauka na mayar da alkalan kan aikinsu bai dace ba. Majalisar Alkalan, inji Sheriff, na iya kawo nakasu ga hukumce-hukumce da zasu zartas a gabansu domin zai yi wuya su yanke hukumci kan laifukan dake kama da nasu. Hakan ka iya kawo raini tsakaninsu da lauyoyi.
Ga rahoton Babangida Jibrin da karin bayani.
Facebook Forum