Kididdiga ta nuna cewa kimanin mutane miliyan bakwai da dubu dari shida ke rasa rayukansu a kowacce shekara a duniya, a sanadin cutar sankara ko daji, an kuma yi hasashen cewa adadin zai iya kaiwa miliyan sha uku nan da shekarar 2030. A Najeriya kadai, cutar na kashe mutane kusan dubu goma a kowacce shekara yayinda kuma ake samun sababbin masu kamuwa da cutar kusan dubu dari biyu da hamsin kowacce shekara.
Masana na ta’allaka karuwar barazanar cutar da karancin ilimi da fadakarwa, da kuma karancin cibiyoyi da na’urorin maganin cutar.
Wannan ya zaburarda da kungiyoyi masu zaman kansu fitowa da shirye-shirye don marawa gwamnati baya wajen yaki da cutar. Mai dakin gwanan jihar Kebbi Dr. Zainab Atiku Baguda na cikin wadanda suka bi sahu wajen fito da wani shiri na yaki da cutar mai suna Medicaid foundation a turance.
Dr. Zainab Bagudu ta ce babbar matsalar da ake fuskanta ita ce rashin fahimtar cutar, don wasu na daukar cutar a matsayin asiri, ko tsafi, ko wani abin al’ajabi. Muhimmancin duba jiki, da cin abinci mai ingaci, da motsa jiki na cikin abubuwan da gidauniyar ke fadakar da jama’a a kai da kuma abin da ya kamata su yi idan sun ga alamun cutar.
Dr surayya Mansu Mohammad ita ce ke shugabantar asusun a Najeriya. Tace cutar na bukatar tallafin ba na gwamna ti kadai ba har ma da na sauran a’lumma, saboda ciwo ne wanda kula da shi da maganin sa na da tsadabayan haka na’urorin da ake bukata suna da karanci musamman a kasarmu na Najeriya. Ta kara da cewa akwai bukatar gwamnati da masu hannu da shuni su yaimakwa masu fama da wannan cutar.
Asusun na Medicaid zai mamaye duk fadin Najeriya, amma a jihar Kebbi ayyukansa zasu fi maida hankali da kuma makwabtan jihohin Sokoto da Zamfara.
Facebook Forum