Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Sojojin Najeriya Sun Kashe ‘Yan Boko Haram 15 da Wasu Kwamandojinsu a Borno


Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai
Hafsan Sojojin Najeriya Tukur Yusuf Buratai

Ta bakin kwamandan sojojin Najeriya dake fafatawa da ‘yan Boko Haram a jihar Borno, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, yayinda yake bayyana irin nasarorin da suke samu a fafatawar da suke yi da mayakan Boko Haram

Kwamandan rundunar sojojin Najeriya dake Maiduguri, Manjo Janar Ibrahim Attahiru, ya tabbatar da hallaka wasu mayakan Boko Haram 15 sakamakon yunkurin da suka yi na kai hari kan sojojin Najeriya dake garin Gwoza a jihar Borno.

A bayanin wata-wata da sojoji ke yiwa ‘yan jarida a garin Maiduguri kan fafatawarsu da ‘yan ta’adda, Manjo Janar Ibrahim Attahiru ya yi cikakken bayani kan nasarorin da suka samu, inda yace wasu ‘yan Boko Haram da suka yi kokarin kai masu hari a Gwoza sun gamu da bala’i inda suka yi kaca-kaca da su, har sojan suka kashe 15 daga cikinsu tare da kwato makamai masu dimbin yawa. Sun kuma kwace wata mota da ‘yan ta’addan suka dana mata bindigar kakkabo jiragen sama.

Kwamandan yace yanzu ‘yan Boko Haram sun fi kai hari kan sansanin ‘yan gudun hijira. Ya kuma tabattarda cewa wasu ‘yan ta’addan su 10 sun mika kansu da kansu yayinda sojoji suka samu kwato wasu mutane 230 daga hannun ‘yan Boko Haram din.

Ga rahoton Haruna Dauda da karin bayani

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:16 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Kamala Harris Ta Amince Da Shan Kaye A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:03 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Sakamakon Zaben 2024 A Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:01:44 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
Masana akan manufofin 'yan takarar biyu na shugaban kasar Amurka a takaice
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG