Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Masu Ruwa Da Tsaki Sun Bayyana Dalilan Da Ke Haifar Da Cinkoso A Gidajen Yari


Duk da damuwar da shugaban kasa Muhammu Buhari ya nuna a game da cunkoson da ake samu a gidajen yarin da ya ce ya kamata a rage, masu ruwa da tsaki a kan harkokin gidajen yarin kasar sun ce ba wani abune ke kawo cunkoso ba illa yadda aka mayar da tura kowane irin kankanen laifi zuwa gidan kaso.

Malam Yazid Bala Alhassan, shine jami’in dake kula da gidan kason dake jihar Kaduna, kuma ya bayyana dalilan dake kawo cunkoso a gidan kaso wadanda suka hada da neman abinci, domin a cewarsa ana ciyar da ‘yan hursuna sau uku a rana lamarin da ya sa wasu da dama sun garace su zauna a gidan yari.

Da yake amsa tambayar da wakilin sahsen Hausa na muryar Amurka Isa Lawal Ikara, ya yi masa akan masu kananan laifin da ake kaiwa gidan kaso ba tare da an sallami wasu ba, shugaban ya bayyana cewa basu da irin wadannan a gidajen yarinsu domin kuwa gwamnatin jihar ta kafa wani kwamiti karkashin kulawar kwamishinan shari’a domin ziyartar gidan yari komai kankantar sa domin rage masu kananan laifuka.

Malam Yazid ya kara da cewa duk da kokarin rage masu kananan laifukan da kwamitin ke yi, har yanzu gidajen kason a cunkushe uke da jama’a sakamakon yawan aikata laifukan da ake, sa’an nan akwai hanyoyin horas da mai laifi kamar su cin tara kokuma zuwa shara a kasuwa da sauransu, duk hanyoyi ne na rage yawan cunkoso a gidajen yari.

Ya kuma kar da cewa wata hanya ta rage wannan matsala ita ce samawa matasa ayyukanyi domin rashin ayyukan yin a daga cikin dalilan da ke sa matasa aikata laifuka, misali wadanda suka koyi sana’ar hannu kamar su aski, gyaran gashi da kwamfuta, da zarar an sallame su daga gidan kaso basa sake komawa.

Barista Muhammad Ibrahim Zaria, masanin shari’a ne kuma lauya ne mai zaman kansa ya bayyana cewa da dama da ya kamata a yi masu shari’a anyi watsi da su, wasu kuma basu da kudin beli.

Domin Karin bayani saurari rahoton Isa Lawal Ikara.

please wait

No media source currently available

0:00 0:04:13 0:00

Facebook Forum

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Nijar Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:47 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Hira Ta Musamman Kan Nasarar Donald Trump Da Kayen Da Kamala Harris Ta Sha
please wait

No media source currently available

0:00 0:04:56 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Shugabannin Kasashen Nahiyar Turai Suka Taya Donald Trump Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:03:55 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA

Zaben 2023

TASKAR VOA: Ra'ayoyin Wasu 'Yan Ghana Kan Nasarar Donald Trump A Zaben Amurka
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:40 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
TASKAR VOA: Yadda Trump Da Magoya Bayanshi Suka Yi Murnar Lashe Zabe
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:27 0:00
Karin bayani akan Rahotannin Taskar VOA
XS
SM
MD
LG