Fadar shugaban Amurka ta White House ta bada labarin cewa shugaba Barack Obama ya aike da wasikun neman goyon baya daga shugabannin kasashen Afirka ta yin kira das u badagoyon bayansu domin samun nasarar kuri’ar raba gardama a Kasar Sudan daza’a gudanar wata mai zuwa.
Mai Magana da yawun majalisar tsaro ta Amurka Mike Hammer jiya lahadi yake cewa shugaba Obama ya aike da wasikun neman goyon bayan ne tare da karfafa cewar Sudan na daya daga cikin muhimman tuwasun gina manufofin hulda da kasaashen Afirka da Amurka ta dogara dasu don haka, shugaba Barack Obama yake gargadin idan ba’a sami nasarar kuri’ar raba gardama cikin kwanciyar hankali wata mai zuwa ba, kasar Sudan na iya sake komawa ga yakin basasa tsakanin Arewa da kudancin Sudan