Gwamnatin Zambia ta bada labarin ba zata kama shugaban Omar al-Bashir na Sudan ba,idan ya halarci taron koli da za’a yi kasar cikin makon gobe.
Wani kakakin gwmnatin kasar, yace Zambia tana mutunta matsaya da Tarayyar Afirka ta cimma, na watsi da sommacin kotun kasa da kasa,mai hukunta manyan laifuffuka,da cin zarafin bil’adama ta bayar kan shugaban na Sudan.
Tarayyar Afirka tace ba’a yankewa shugaban na Sudan wani hukunci ba, saboda haka babu dalilin kama shi.
Shugaban na Sudan bai fito fili ya bayyana ko zai halarci taron na makon gobe ba.