Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Gwamnatin Shugaba laurent Gbagbo a Ivory Coast Ta Bukaci Sojojin Kiyaye Zaman Lafiya na Majalisar DinkinDuniya,Da Na Faransa Su Bar Kasar Ba Tareda Bata Lokaci Ba.


Motocin Sulke na sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Ivory suke tsaye kusa da O'tel da Mr. Ouattara yake aiki daga ciki.
Motocin Sulke na sojojin kiyaye zaman lafiya na Majalisar Dinkin Duniya a Ivory suke tsaye kusa da O'tel da Mr. Ouattara yake aiki daga ciki.

Magoya bayan Mr.Gbagbo suna zargin dakarun kiyaye zaman lafiya da taimakawa abokin hamayyarsa Alassane Ouattara. kakakin Mr. Gbagbo ta gayawa tashar talabijin ta kasar cewa rundunar ta kaucewa kai'dojin aikinta.

Gwamnatin Ivory Coast, ta shugaba Laurent Gbagbo, ta bukaci sojojin Majalisar Dinkin Duniya da na Faransa su bar kasar ba tareda bata lokaci ba.

Magoya bayan Mr. Gbagbo, suna zargin sojojin kiyaye zaman lafiya da taimakawa abokin hamayyarsa Allassane Ouattara.Da take magana a tashar talabijin kasar,wata kakakin Mr. Gbagbo,tace rundunar kiyaye zaman lafiyar ta kaucewa ka’idojin aikinta.Haka kuma tace gwmnatin Mr. Gbagbo tana adawa da duk wani kokarin sake sabunta wa’adin rundunar da zai kare ranar litinin.

Majalisar Dinkin Duniya da jami’an Faransa, duk basu mai da martani nan nan da nan kan wan nan yunkurin ba.

Mr. Gbagbo yaki amsa kiraye kirayen Majalisar Dinkin Duniya,Faransa,Tarayyar Afirka,da wasu suka yi masa na mika iko ga Mr.Ouattara,mutuminda kasashen Duniya suka yi amannar shine ya lashe zaben fidda gwani na shugaban kasar da aka yi cikin watan jiya.

Ita dai Majalisar Dinkin Duniya tana da sojojin kiyaye zaman lafiya dubu 10 a Ivory Coast,darururuwa daga cikinsu suna bada kariya a O’tel din da Mr.Ouattara yake aiki daga ciki a matsayin sakatriyat dinsa.

Faransa tana da kimanin sojoji 900 cikin kasar dake yammacin Afirka.

XS
SM
MD
LG