Zata fitar da mutum daya daga cikin mutane biyar da suka nuna sha'awarsu.
Taron za'a yishi ne bayan rassan jam'iyyar a duk jihohin Najeriya suka kammala tacewa da fitar da 'yan takaran gwamnoni, majalisun tarayya da na jihohi. Taron Legas zaben dan takarar shugaban kasa kawai zasu yi.
Malam Nasiru Isa Abubakar shugaban jam'iyyar a jihar Katsina yace an kammala duk shirye-shirye da bin ka'ida da yadda za'a samu masalaha a wurin zaben ba tare da an samun korafe-korafe ba.
Dangane da gujewa korafin yin magudi Malam Nasiru yace idan Allah ya yadda zasu tantance masu tsayawa zabe. Su kuma masu kada kuri'a kowa za'a bashi damar ya zabi wanda yake so. Zasu ajiye akwatuna kamar ashirin kana a dinga zuwa jefa kuri'a jiha jiha. Sai jiha ta gama kafin wata jihar ta fito. Akwatunan basu da sunan kowane dan takara. Sai an gama jefa kuri'u kana a kirgasu. Bayan an kirgasu za'a ware na kowa daban daban. Za'a sake kirgawa a fadi adadin da kowa ya samu a cikinsu. Wakilansu zasu tabbatar cewa abun da aka yi daidai ne. Za'a rubuta a takarda kowa ya sa hannu kafin a yi shela.
Dangane da illar da yin anfani da kudi zai yiwa dimokradiya yace hakika ana anfani da kudi amma mafi yawan masu zabe a Najeriya kansu ya waye. Suna iya karbar kudin mutum amma su ki zabensa.
Ga karin bayani.