Alhaji Atiku Bagudu ya fafata ne da 'yan takara hudu a zaben fidda gwani na dan takarar kujerar gwamnan jihar Kabbi a karkashi inuwar jam'iyyar APC.
Sanata Bagudu yayi rinjaye tare da tazarar gaske. Da ma can Sanata ya nemi tsayawa takarar gwamna a jam'iyyar PDP kafin ya canza sheka makon jiya tare da wasu jigajigan 'yan PDP a jihar.
Muryar Amurka ta tambayeshi abun da zai yi yanzu da yake ta tabbata cewa zai fuskanci dan takarar PDP a zaben gwamna. Yace bashi da wata kalubale wurin fuskantar dan takarar PDP domin 'yan jam'iyyar da yawa suna da damuwar da suka sa shi da wasu suka barta. Yace PDP ba zata biyawa mutanensa bukata ba kamar yadda ta fara da can.
To saidai zaben na APC a Kebbi ya bar baya da kura. Tuni wasu 'yan takarar suka yi korafin rashin adalci a gudanar da zaben na dan takarar gwamna da wasu mukamai.
Habeeb Adamu Argungu wakilin Dr. Yahaya Argungu yace an shirya zabe da misalin karfe daya na dare amma ba'a yi ba sai karfe uku na yamma. Sai da suka shirya komi kana suka kawo wasu wakilai daban domin su shirya zaben. Dr Ismaila Ahmed Muhammed mai takarar kujerar majalisar wakilan tarayya yace tun safe suka fito domin zaben amma suna kaiwa da kawowa babu abun da aka yi. Amma wai suna jin raderadin ana son a yi masu dauki dora.
Amma daya daga cikin shugabannin jam'iyyar APC a jihar Sani Jauro Hukuma dangane da korafe korafen. Yace su 'yan jam'iyyar APC suka bido Atiku ya zo ya tsaya takara domin ya cancanta. Ya kuma shaida Atiku bai baiwa kowane wakili kudi ba.
Ga rahoton Murtala Faruk Sanyinna.