WASHINGTON, DC —
A wani taron manema labarai jam'iyyar APC ta zargi PDP da shirin yi mata zagon kasa ta hanyar kulla mata rikicin cikin gida.
Mataimakin shugaban jam'iyyar APC na kasa mai kula da bangaren arewa maso gabas Dr. Umar Duhu shi ya bayyana hakan a taron manema labarai. Ya ce PDP na kokarin kawo hargitsi da rudani cikin jam'iyyarsu.To amma PDP ta musanta zargin. Dr. Duhu ya ce suna sane da wadanda ake son a yi anfani dasu domin raba kawunan 'ya'yan jam'iyyar. Shirin ya fi karfi a jihohin da gwamnoninsu suka koma APC. Ya sha alwashin ba zasu kyale batun ba. Ya ce duk abun da PDP keyi kan mage ya waye. Talakawa suna gani kuma sun sani.
A nasu martanin PDP tace zargin APC tamkar tatsuniya ce. Alhaji Gombe kusa cikin jam'iyyar PDP a jihar Adamawa ya ce APC ba zata kai labari gida ba. Hayaniyarsu dake cikin gidansu kadai ta ishesu. Amma su a PDP suna nan daram. Babu gudu babu ja da baya. Ya ce a fada mashi abu guda da PDP ta ce ko wani dan PDP ya ce masu. Duk abun da su keyi tsakaninsu ne. Ya ce su tsaya su dinke hayaniyar dake cikinsu kafin su hango PDP.
Masana harkokin siyasa irinsu Umar Dan Kano ya ce shekarar 2014 shekarar siyasa ce. Ya ce PDP tana kokarin ta shirya 'ya'yanta yadda zata cigaba da mulki. Ita ko APC tana neman yadda zata kai ga kwato mulki daga hannun PDP ne. Yanzu kowa na kokari ne. Iya ruwa iya fitar da kai.
Ga karin bayani.