WASHINGTON, DC —
A jihar Gombe Haruna Goje tsohon gwamnan jihar bai samu goyon bayan manyar jam'iyyar APC ba domin haka sun ki shi a matsayin daya daga cikin shugabanninsu na kasa.
Abubakar Aliyu wanda ya yi takarar gwamna karkashin jam'iyyar CPC a zaben shekarar 2011yana cikin shugabancin APC a jihar. Ya ce suna cikin shirin zabo shugabanni sai kwatsam an saka sunan Haruna Goje cikin shugabannin kasa wanda tsohon gwamnan jihar ne kuma daga PDP ya fito. Ya ce bugu da kari sai Goje ya kira taro na 'yan Gombe a Abuja. Ya ce shi ya ki zuwa taron domin idan taron da ya shafi Gombe ne to a Gombe ya kamata a yi shi. Ba za'a dauki al'amarin Gombe a baza shi a Abuja ba. Kuma duk abun da suka yi a Abuja ya ce shi bai yadda da shi ba.
Abun da suke so shi ne a bi ka'ida. A bi dimokradiya. A yiwa mutane adalci.Kada a yi nadi irin wanda PDP ta saba yi.
Sai dai Keften Bala Jibril kakakin jam'iyyar APC a jihar Gombe ya ce ba za'a bari takaddama dake tsakanin Abubakar Aliyu da Haruna Goje ta shafi jam'iyyarsu ba. Ya ce zasu zauna sai sun samu masalaha. Banda Abubakar Aliyu da Haruna Goje akwai wasu ma amma za'a zauna a daidaita. Ya ce su bakwai ne shugabanni daga yakin arewa maso gabas. Zasu zauna da yadda Allah su kawo sulhu a jihar Gombe da ma sauran jihohin.
To saidai kawo yanzu Haruna Goje tsohon gwamnan jihar ta Gombe bai fito fili ba ya ce yana jam'iyyar APC.
Ga karin bayani.