Yanzu da alamu wasu kusoshin PDP dake majalisar dattawan kasar zata tsunduma cikin APC. Dan majalisar wakilai Ado Doguwa daga jihar Kano da ya bi ayarin wasu suka canza sheka zuwa APC ya bada tabbacin hakan zai faru a dunkule. Ya ce cikin satin farko ko na biyu na sabuwar shekara akwai babban jirgi na amir haji da zai sauka. Yana nufi wasu 'yan PDP da yawa zasu shiga APC. Mutanen da zasu shiga APC zasu san cewa rigimar da suka fara da PDP bata wasa ba ne. Ado Doguwa ya ce jam'iyyar PDP ta riga ta mutu a Najeriya.
Domin dakile fita daga PDP ya sa jam'iyyar ta yi tayin ba 'yan jam'iyyar zarcewa a zabe mai zuwa ba hamayya. Sai dai abun mamaki shugaban jam'iyyar Bamanga Tukur yana ganin har yanzu tagomashni jam'iyyar na nan daram. Bamanga ya tsaya kan shugaba Jonathan zai ci zabe duk da abubuwan dake faruwa a jam'iyyar. Irin wannan matsayin nasa ya sa duk da yadda jam'iyyarsa ke ramewa ya sa 'yan hamayya suke yaba masa. Suna ganin tamkar ma yana rage masu dawainiyar tinkarar PDP ne. Buba Galadima dattijon APC ya ce ai basu da wani babban malami ko boka wanda yake taimakawa 'yan hamayya kamar Bamanga Tukur. Ya ce sun sayeshi ne kuma sun biya domin ya ruguza PDP kuma yana yi. Ya ce idan ba mutumin dake tausayawa jam'iyyun adawa ba babu wanda zai yi irin abubuwan da Bamanga Tukur ya keyi.
To sai dai wata ta ce ko maza sun kaucewa Jonathan mata zasu mara masa baya domin ya zarce. Binta Kuraye daga Katsina kurarin da ta yi kenan. Ta ce idan wasu kudi Obasanjo ya ke cewa Goodluck Jonathan ya ci to ai kafin ya cisu Obasanjo ya rigashi. Ta ce a lokacin da Obasanjo yake mulki ya ce jiragen ruwa shida dauke da danyan man fetur sun bace cikin teku. Ta ce bayan sun dan yi rufa-rufa sai aka kamo wasu bayan 'yan kwanaki kuma aka sakesu. Haka maganar ta mutu.Ta ce ai Googluck bai taba kamanta irin wannan ba. Ta ce an tsargi Goodluck ne domin shi ba dan arewa ba ne kuma ba Musulmi ba ne. Amma ta ce su mata suna son Jonathan kuma suna son ya wuce. Ta ce duk da tsangwama da masifa da a keyi masa Allah yana iya maido da Jonathan a shekarar 2015.
Masu harsashe na ganin shugana majalisar dattawa zai koma APC domin kare kujerarsa. Sai dai mataimakinsa Ikwere Madu na kokarin kawo wani kuduri da zai karawa shugaban kasa da masu rike da mukamai wa'adin shekara biyu. Idan lamura suka daidaita a yi zabe a shekarar 2017 ba 2015 ba
Ga rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya.