Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Tuhumar Wani Mutumin Jihar Arizona Da Laifin Safarar Bindigogi Don Kashe Bakar Fata


Mark Adams Prieto
Mark Adams Prieto

An tuhumi wani dan jihar Arizona bisa laifuka hudu da suka shafi safarar bindigogi bayan da masu gabatar da kara na gwamnatin tarayya suka ce wani samame da aka gudanar a boye ya nuna cewa ya shirya kashe bakaken fata a wani harin da ya ke da nufin gudanarwa, a cewar tuhumar.

Wani babban alkali ya gurfanar da Mark Adams Prieto mai shekaru 58 a ranar Talata bisa zarginsa da laifin safarar bindigogi domin amfani da su wajen aikata laifin nuna kyama da kuma mallakar bindiga mara rajista.

An tsayar da Prieto ne a ranar 14 ga Mayu yayin da ya ke tuki kan babbar hanyar New Mexico inda aka kama shi da bindigogi bakwai a cikin motarsa, a cewar ofishin da ke wakiltar gwamnatin Amurka na gundumar Arizona.

Tun da farko dai ya shaidawa wani jami’in hukumar FBI da ya fake a matsayin mai son nuna wariyar launin fata cewa ya shirya ya tuka mota zuwa birnin Atlanta na jihar Georgia domin leken asirin wuraren da za a iya kai wa hari, da nufin aiwatar da harin gabanin zaben shugaban Amurka a watan Nuwamba, a cewar tuhumar da ake masa.

Tsakanin watan Janairu da Mayu, Prieto ya gana akai-akai tare da wani jami'in sirri na FBI da wata majiya mai taimakawa FBI a asirce don nunin bindigogi daban-daban a kusa da Arizona.

Kafin watan Janairu, ya yi magana da jami’in FBI din da ke fake game da "kai harin kan Bakar fata, da Musulmai, da Yahudawa" a cewar karar.

Prieto ya shirya halarta wani bikin kide-kide a birnin Atlanta inda dimbim Amurkawa bakar fata za su halarta domin gudanar da harin.

Sai dai makonni kadan bayan haka, a wani wasan nuna bindiga a Phoenix, Prieto ya shaidawa jami'in FBI din cewa yana tunanin canza wurin harin zuwa masallaci, in ji karar.

Yanzu haka yana fuskantar hukuncin daurin shekaru 15 a gidan yari idan aka same shi da laifi..

Ba a samun jin ta bakinsa ba, yayin da lauyan da ke wakiltarsa bai amsa tambayoyin nan da nan ba.

Dandalin Mu Tattauna

XS
SM
MD
LG