Fadar shugaban Amurka ta White House tace tana sa ran tattaunawar wuni biyu tsakanin shugaban Amurka Donald Trump da takawaran aikin sa na Japan Shinzo Abe, "zata yi tasiri sosai."
Da take yiwa manema labarai bayani a cikin jirgin saman shugaban Amurka da ake kira "Airforce One" da turanci, sakatariyar yada labarai ta fadar White House Sarah Huckabee Sanders, tace tattaunawar shugabanin biyu zata fi maida hankali ne a kan shirye shiryen ganawa da shugaban Koriya ta Arewa, da kuma batutuwan da suka shafi cinikaiya.
Trump da Abe ba bakin juna ba ne. Firayim Ministan Japan shine shugaban wata kasa da shugaban na Amurka ya gana dashi kuma ya sha magana dashi tun zamansa shugaban Amurka.
Mr Trump da Abe suna da matsala guda,watau Koriya ta Arewa, wacce ta mallaki makamai masu linzami, da shirin Nukiliya wadda hakan ya sa ta bijirewa takunkumin da hukumomin kasa da kasa suka kakaba mata.
Masu sharhi sun ce shugaba Abe zai yi kokarin shawo kan shugaba Trump cewa idan ya gana da shugaba Kim, kada ya kulla wata yarjejeniya da Koriya ta Arewa, wacce zata raunata tsaron Japan, dake karkashin shirin laimar tsaron nukiliyar Amurka, kana kuma take zaman mai masaukin dubban sojojin Amurka.
Facebook Forum