A dai dai lokacinda Rasha take kashedin cewa yaki na iya barkewa tsakaninta da Amurka kan Syria, shugaba Donald Trump ya kira taron majalisar tsaro domin tataunawa kan martanin da Amurka zata dauka dangane da harin baya-bayan da makamai masu guda da ake aza zargin akan dakarun Syria dake biyayya ga shugaba Bashar al-Assad.
Kamin ya fara taron da manyan masu bashi shawara kan harkokin tsaro da soja, shugaba Trump yace za'a yanke shawara "nan ba da jumawa ba."
Rasha ta kira ga duka sassa dake da hannu a rikicin na Syria su guji daukan matakai da zasu kai ga janyo rudani ko-daka iya wargaza yankin.
"Muna fata cewa ba za'a kai ga matsayin babu halin janyewa ba, cewa Amurka da kawayenta zasu guji daukar matakin soja kan kasa mai diyauci. A fahimci hadarin rikicin nan ya ruruta yafi yawa domin wannan ba Syria ce kawai ba, sojojin mu suna kasar bisa gayyatar gwamnatin Syria, Inji Jakadan Rasha a Majalisar Dinkin Duniya, MDD, Vassily Nebenzia.
Facebook Forum