Wannan ne karon farko da za’a fafata babbar gasar Tennis ta Grand Slam, tun sa’adda annobar coronavirus ta dakatar da al’amura a fadin duniya.
Zaratan ‘yan wasa da dama ba za su fafata gasar ta bana ba, duk da yake dai akwai shahararrun ‘yan wasa da suka hada da Novak Djokovic, Serena Williams da Andy Murray.
Za’a fafata gasar ta bana ne ba tare da ‘yan kallo ba kamar yadda aka saba sakamakon annobar ta coronavirus, haka kuma za’a gudanar da gasar ne cikin tsauraran mataka kariya, da suka hada da gwajin cutar akai-akai ga ‘yan wasa da kuma takaita zirga-zirgarsu, da ta jami’ansu da ma hukumomin shirya gasar.
Mai rike da kambun gasar a bangaren maza Rafael Nadal da Bianca Anddreescu, da kuma Roger Federer, na daga cikin zaratan ‘yan wasan da ba za su fafata gasar ta bana ba sakamakon matsalolin rashin lafiya da suke fama da shi.
Haka ma za'a yi kewar mace ta farko a duniyar Tennis Ashleigh Barty da kuma zakarar Wimbledon Simona Halep, wadanda su ma za'a fafata gasar ta bana ba tare da su ba.
Facebook Forum