A Libya,kazamin fadan da ake gwabzawa tsakanin dakarun da suke biyayya ga gwamnatin kasar da kuma mayakan sakai masu ikirarin Islama a Benghazi cikin ‘yan kwanaki da suka wuce ya halaka akalla mutane 65.
Fadan ya tilastawa dubban mazauna birnin na biyu a girma a gabashin kasar, su kauracewa muhallansu.
Wannan tashe tashen hankulan yana zuwa ne a lokacinda kasar take cika shekaru uku da kamawa da kuma kisan stohon shugaban mulkin kama karya na kasar Moammar Gadhafi. Amma kasar tana cikin yamutsi, inda mayakan sakai masu ikirarin Islama da suka kafu daga kungiyoyin da suka yi adawa da gwanatin Gadhafi suka fara fada domin iko kan yankunan kasar, sojojin gwamnati kuma basu da karfin taka musu birki.
Ranar Asabar Amurka tare da Britaniya da Faransa, da Jamus da Italiya suka yi kira na kawo karshen tashe tashen hankulan nan take.
Ahalinda ake ciki kuma, dan kasar Libyan nan Ahmed Abu Khattala, jiya Litinin, yaki ya amsa laifi a gaban wata kotun Amurka kan zargin yana da hanu a harin da aka kai kan karamin ofishin jakadancin Amurka a Benghazi wanda ya hallaka Amurkawa uku ciki harda jakadan Amurka, da aka kai ranar 11 ga watan satumba shekara ta 2012.