Maniyattan sun bayyana irin wahalolon da suka ci karo dasu a kasa mai tsari yayin da suke aikin hajjin bana.
Alhazan da suka tafi daga jamhuriyar Niger su 12,702 ne amma duk da haka sun yi zargin kasawar hukumar alhazan kasar. Sama da dubu bakwai sun dawo cikin koshin lafiya kana sauran suna baya.
Da yawa cikin alhazan sun ce basu gamsu ba da yadda hukumar alhazai ta kasa ta kula dasu a kasar Saudiya tare da kamfanonin dillancin sufurinsu.
Wani da bai yadda a ambaci sunansa ba yace sun hsa wahalhalu da dama a kasar. Yace sun biya kudin abinci da na kwana amma idan mutum ya tashi akan dan'uwansa zai fada sabili da rashin isasshen wurin kwanciya. Ko da suka je hawan Arafa sai da suka nemi abinci da kansu. Hukumar alhazan ta kasa, ko kulawa da mutane bata yi.
Bugu da kari alhazan sun koka da rashin samun ingantacen kiwon lafiya wanda nauyi ne da ya rataya a wuyan hukumar alahazai. Sun kuma sha tsadar zuwa hajji bana. Dangane da tsadar ana nuna yatsa akan kamfanonin sufurin kasar Niger.
Alhaji Muhammed Fari daraktan daya daga cikin kamfanonin dake dillancin alhazai yace aikin hajji ba aikin zuwa jin dadi ba ne. Dole mutane su hade wuri guda kamar ciyawa. Ana cunkoso wuri guda maza da mata. Mutum baya cewa yana neman wurinsa domin ya ya ji dadi. Duk duniya haka ake game. To amma saura sai su ware su je su zauna wani wuri. To idan an zo raba abinci mutumin da ya fita ba za'a nemoshi a bashi ba. Wanda duk ya bar inda alhazai suke ba za'a nemshi da abinci ba.
Mahukunta sun kafa wani kwamiti domin warware matsalolin da alhazai ke fuskanta.
Ga rahoton Abdullahi Mamman Ahmadu.