Ofishin jakadancin Amurka a kasar Ethiopia na kashedin cewa akwai yiwuwar kai harin ta'addanci a wani sashen Addis Ababa babban birnin kasar.
Ofishin jakadancin ya ce ya samu rahotannin cewa kungiyar al-Shabab ta 'yan tawayen kasar Somaliya ta kudiri aniyar kai hari wani unguwar Bole, a kudu maso gabashin birnin Addis Ababa.
Wata sanarwar da ofishin jakadancin na Amurka ya gabatar ba ta ce ga inda za a kai harin da ake zaton kaiwa ba, amma dai sanarwar ta ce ya kamata a kiyayi zuwa gidajen cin abinci, da otel-otel, da wuraren ibada, da kantuna da kasuwannin dake yankin unguwar ta Bole, har zuwa wani lokaci saboda irin wadannan wurare ake iya kaiwa harin ta'addanci. Haka kuma sanarwar ta hori Amurkawa da su guji duk inda suka ga taron jama'a, da kuma wuraren shakatawar da 'yan kasar Ethiopia da kuma Turawa ke yawan zuwa.
Ethiopia na cikin kasashen Afirka dake da sojojin su a kasar Somaliya su na yakar 'yan al-Shabab.
Baya-bayan nan kungiyar ta al-Shabab ta ji jiki, a ciki har da mutuwar shugaban ta a harin da Amurka ta kai da wani jirgin ta na yaki da ba matuki a ciki, amma duk da haka kungiyar na ci gaba da kai munanan hare-hare masu kisa.
A shekarar da ta gabata kungiyar al-Shabab ta kai hari kan wata cibiyar hada-hadar kasuwanci ta kasar Kenya inda mutane 67 a kalla suka mutu.
A bana sau biyu kungiyar na kai hari kan fadar shugaban kasar Somaliya a birnin Mogadishu.