Ma'aikatar harkokin wajen Turkiyya tace hukumomi zasu gudanar da bincike a karamin ofishin jakadancin Saudi Arebiya dake Santanbul, biyo bayan bacewar wani Dan-Jaridar kasar Saudiyya, Jamal Khashoggi.
Wata sanarwar da ma’aikatar ta Saudiyya ta fitar, ta nuna alamun a shirye take ta bada hadin kai, amma dai ba a tabbatar da lokacin da za a soma gudanar da binciken ba.
Ba a sake ganin Mr. Khashoggi ba tun bayan shigar shi ofishin a makon da ya gabata, hukumomin Turkiyya sunce an kashe shi a cikin ofishin. Amma gwamnatin Saudi Arebiya, tace ya bar ofishin lafiya.
Duk da haka, shugaban kasar Turkiyya Tayyip Erdowan, yace akwai bukatar Saudi Arebiya, ta bada bayanai gamsassu na cewar ya fita daga ofishin, a ranar Talatar makon jiya, a lokacin da yaje don karbar takardun auren shi, da yake shirin yi da wata ‘yar kasar Turkiyyar. Matar da zai aura Hatice Sengiz, tace ta jira shi a bakin ofishin amma bai fito ba.
Facebook Forum