Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Turkiyya Na Zargin Saudiyya Da Kashe Danjarida Jamal Khashoggi


Jamal Khashoggi
Jamal Khashoggi

Da alamar dai kasar Saudiyya da kasar Turkiyya za su saka wando guda, bayan da Turkiyya ta zargi Saudiyya da kashe dan jaridar Saudiyya mai gudun hijara a Amurka mai suna Jamal Khashoggi.

Jami'an gwamnatin Turkiyya sun yi imanin cewa, kashe dan jaridar Saudiyya mai gudun hijira a Amurka dinnan aka yi, a makon jiya a karamin ofishin jakadancin Saudiyya da ke birnin Istanbul.

To saidai jami'an gwamnatin Saudiyya sun ce wannan zargi ne mara tushe, duk da yake an daina jin duriyar dan jaridar, wato Jamal Khashoggi dan shekaru 59 da haihuwa.

Budurwar Khashoggi, Hatice Cengiz, wadda ta jira shi a harabar karamin ofishin jakadancin Saudiyya din ranar Talata, ta ce sam bai fito daga ginin ba tun da ya shiga.

Shugaban Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya gaya ma manema labarai ranar Lahadi cewa, "Ina bin diddigin al'amarin kuma za mu gaya ma duniya sakamakon binciken da aka yi a hukumance." Ya kara da cewa, "Da yaddar Allah, ba za mu fuskanci al'amarin da ba mu so ba."

Erdogan ya ce 'yansanda na nazarin faye-fayen bidiyon tsaro da ke mashigar karamin ofishin jakadancin da kuma na filin jirgin saman Istanbul.

'Yan sanda sun ce wasu 'yan Saudiyya kimamin 15 su ka iso birnin Istanbul ta jiragen biyu ranar Talatar da ta gabata, kuma sun kasasnce a karamin ofishin jakdancin Saudiyya din a daidai lokacin da shi ma Khashoggi ya ke ciki.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG