Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

Ana Ci Gaba Da Aikin Ceto Sauran Dalibai Hudu Da Aka Yi Garkuwa Da Su A Jihar Nasarawa


'Yan sandan kwantar da tarzoma a Najeriya
'Yan sandan kwantar da tarzoma a Najeriya

Hukumomin Najeriya sun ce tawagar masu bincike na neman ‘yan bindigar da suke rike da dalibai hudu cikin shida da aka yi garkuwa da su a makarantarsu ranar Juma'a a jihar Nasarawa

Kwamishinan ‘yan sandan jihar Nassarawa, Maiyaki Mohammed Baba, ya shaidawa Muryar Amurka cewa, tawagar da suka hada da sojoji, dan ‘yan sanda da Civil Defense da kuma jama’ar gari, suna gudanar da bincike a wani dajin da ke kusa da jihar, a rana ta biyu da garkuwa da daliban.

Tun farko dai ranar Juma’a ne wasu mutane dauke da makamai suka kai hari a makarantar firamare ta karamar hukumar Alwaza, da ke gundumar Doma a lokacin da yaran ke zuwa makaranta suka yi garkuwa da dalibai shida.

Galibi gungun ‘yan bindiga na kai hare-hare ga makarantu don neman kudin fansa, wadanda suka yi kaurin suna a tsakiya da arewa maso yammacin Najeriya.

Maiyaki ya ce, hukumomin jihar sun kuma karfafa tsaron makarantu don hana sake afkuwar lamarin.

A ranar Asabar din da ta gabata ne jami’an tsaro suka kubutar da ‘yan matan biyu da aka sace tare da sada su da iyalansu bayan an duba lafiyarsu. Maiyaki dai ya zanta da Muryar Amurka ne ta wayar tarho.

Ya ce “Ya zuwa yanzu muna ci gaba da kokarin ganin mun kubutar da sauran, duk suna cikin daji a halin yanzu ana bin wadanda ake zargin, mun samar da masu gadi a dukkan makarantunmu domin ganin irin wannan abu bai sake faruwa ba.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi kiyasin cewa an yi garkuwa da dalibai sama da 1,500, akasarinsu a arewacin Najeriya, tun daga karshen shekarar 2020. Akasarinsu an sako su ne ta hanyar tattaunawa, amma ana ci gaba da tsare wasu.

Har ila yau manoma da makiyaya sun sha yin arangama kan filaye da karancin albarkatu a jihar Nassarawa.

Hukumomin Najeriya sun yi ta kokarin ganin sun dakile tashe-tashen hankula makwanni kadan gabanin zaben da aka shirya yi a ranar 25 ga watan Fabrairu, batun tsaro ya kasance babban batu a tsakanin masu yakin neman zabe.

XS
SM
MD
LG