Kuma wannan na zuwa ne yayin da gwamnatin jihar ke yunkurin tada komadar al’ummomin da rikicin ya shafa.
An dai dora laifin bullar Polio a jihar Borno ne cikin kwanakin nan, a kan halin rashin tsaron da ake fama da shi, abinda ya sa ake fuskantar matukar wahala wajen gudanar da ayyukan rigakafi ga wadanda ke cikin hatsarin kamuwa da cutar.
Ministan lafiya na Najeriya Dr Isa’ac Adewole a taron sanar da daukar matakin rigafi a dukkan jihohin arewa ya bayyana cewa a zagaye na farkon rigakafin, sun dukufa ne a jihar Borno inda aka gano wasu yara dake dauke da cutar, sa’annan sai suka shiga jihohi biyar na yankin Arewa maso gabas, yanzu kuma za’a fara a jihohi goma sha takwas.
Ministan ya ce Najeriya na bukatar alluran rigakafi miliyan dari uku duk da cewa kawo yanzu akwai guda miliyan dari a kasa wadnda zasu isa zagaye na farko a riga kafin.
Hajiya Binta Adamu Bello ita ce babbar sakatariyar ma’aikatar lafiya ta Najeriya ta yi Karin bayani akan shirin da ya biyo bayan gano cutar shan inna a wasu kananan hukumomi dake jihar Borno, musamman Goza, inda fitinar boko haram ta dakile ayyukan yiwa yara rigakafin.
Domin Karin bayani ga cikakkun rahotannin Ibrahim Abdul’aziz daga Yola da kuma Nasiru Adamu Elhikaya daga Abuja.