Shedun gani da ido a Nigeria sunce wasu 'yan bindiga sun kaiwa wani ofishin yan sanda a Misau arewa maso gabashin Nigeria hari, har suka kashe akalla mutane biyar.
Shedun, sunce maharan sun yi harbi da bindigogi masu sarrafa kansu, suka kuma tada bama bamai a ofishin yan sanda a garin Misau. Sunce an kashe yan sanda guda hudu da akalla farar hula guda daya.
Mazauna garin sunce ana ta jin karajin harbe harben manyan bindigogi a cikin garin a jiya litinin lokacinda aka kai wannan harin. Jami'an yan sanda sun tabbatar da aukuwar harin, amma basu bada wani karin haske ba.
Ba'a dai tantance ko su wanene suka kai harin ba, amma tarzomar ta yi kama da hare haren da yan kungiyar boko haram ke kaiwa.
An dai dorawa kungiyar boko haram laifin kai hare haren bama bamai da harbe harben da ake auna jami'an gwamnati da yan sanda da kuma Malamai a arewa maso gabashin Nigeria.
Idan ba'a mance ba, kungiyar ta boko haram tayi ikirarin cewa ita keda alhakin harin da aa kai ofishin Majalisar Dinkin Duniya a Abuja, baban birnin taraiyar Nigeria.