‘Yan majalisar dokokin kasar Pakistan sun zabi Shahid Khaqan Abbasi a matsayin sabon Firayin Ministan kasar yau Talata, don maye gurbin Nawaz Sharif, wanda yayi murabus cikin makon da ya gabata, biyo bayan wani binciken rashawa da aka yi.
Abbasi, wanda tsohon ministan man fetur ne, ya dade yana zaman daya daga cikin na hannun daman Sharif. Daman an sa ran cewa bada wata wahala ba zai yi nasara a zaben da majalisar kasar mai kujeru 342, wadda jam’iyyar su Sharif ta Muslim League-Nawaz mai rinjaye ciki, zata gudanar.
Ana sa ran Abbasi zai zama firayin ministan wucingadi kafin kanin Sharif, Shabazz, babban ministan lardin Punjab, ya lashe zaben cike gurbin majalisar. Amma shugabannin ‘yan jam’iyyar adawa sun caccaki wannan salon siyasar akan cewa ya sabawa dimokradiyya.
Sharif dai yayi murabus ne bayan da wata babbar kotu a Pakistan ta gano cewa bai sanarda ‘yan kasar akan albashin wata-wata da ya jima yana karba daga wani kamfani dake Dubai ba, wanda mallakin dansa ne. Hukuncin na zaman wani bangaren binciken rashawa da ake zargin iyalinsa da shi.
Facebook Forum