‘Yan sandan Nigeria sun aza laifin tada boma-bomai biyu a kan ‘yan kungiyar “Boko Haram”, kungiyar da sama da shekaru biyu ke nan take adawa da yaki da jami’an tsaro da hukumomin Nigeria bisa niyyarta wajen ganin kafuwar kasa mai bin tafarkin Islama bai daya a Nigeria.
Amma, a wata sanarwar da kungiyar ta “Boko Haramun” ta bayar ran lahadi, ta kare manufarta wajen kaiwa ‘yan sanda da shugabannin addini hari inda take cewa suna hada baki ne da Gwamnatin tarayya wajen bata mata suna da kagen cewa wai kungiyar tana kokari ne ta lalata tuwasun Islama.Ga dukkan alamu, hare-haren bom din na baya-bayan nan basu da alaka da tashe-tashen hankulan da suka biyo bayan sakamakon zaben shugaban kasar da aka yi makon jiya. Rikicin da kungiyar kare hakkin Bil Adama ta Nigeria tace akalla mutane dari biyar ne suka halaka. Ita kuwa hukumar agajin gaggagwa ta Nigeria tace jihohin Nigeria da suka fi cutuwa daga rikice-rikicen siyasar makon jiya sun hada da Kano, Kaduna,Bauchi,Adamawa, Niger, da kuma Katsina. Babban darektan hukumar bada agajin gaggawa ta Nigeria Muhammad Sani Sidi yace yanzu haka hukumar na tallafawa mutane sama da dubu 21 da suka galabaita a Kano, sannan mutanen da yawansu ya kusa kaiwa dubu goma sun rasa muhallinsu a Zaria, kuma farar hula guda dari ake lura dasu a Kaduna.