Accessibility links

Labari da Dumi-Duminsa

An Yi Yekuwan Nemarwa Kananan Hukumomi ‘Yanci A Abuja


Zanga Zangar malamai a Abuja
Zanga Zangar malamai a Abuja

Kungiyar Malaman Makarantu a Najeriya ta shiga rukunin masu goyon bayan a baiwa kananan hukumomi cin gashin kai. Hakan ya baiyyana ne a lokacinda suka yi zanga zanga ta mussaman a Abuja.

Yekuwan nemarwa kananan hukumomi ‘yanci yana da dumbin tarihi a Najeriya, tun daga zamanin taron kasa na Vision 2010 zamanin mulkin marigayi Sani Abacha da aka gudanar a shekarar alib da dari tara da saba’in da bakwai da taron kasa na gwamnatin Olusegun Obasanjo, a shekarar dubu biyu da biyar, da na gwamnatin Goodluck Jonathan a shekarar dubu biyu da goma sha hudu, da kuma sake tsarin kundin tsarin mulkin kasa da majalisar dokokin tarayya tayi karkashin jagorancin mataimakin shugaban majalisar dattijai Ike Ikweremadu. Da kuma tarruruka da yekuwa daga kungiyoyi da dama.

Daruruwan malamai da suka yi zanga zangar sun zaga birnin tarayya Abuja, dauke da kwalaye dake nuna goyon bayansu, game da ‘yancin kananan hukumomi, amma suka ce a kyale hidimarsu ta ci gaba da kasancewa karkashin jihohi.

Masu zanga zangar sun bayyana takaicin ganin hukumomin jihohin suna karkatar da albashin ma’aikatan kananan hukumomi da ake basu zuwa gudanar da wadansu ayyuka na dabam. Bisa ga cewarsu, kasancewa mulki yana hannun gwamnoni, basu damu su kori malamai ba.

Masu zanga zangar sun yi kira da a cire harkar malamai daga karkashin ikon gwamnatin jihohi idan ana son ci gaban ilimi a wannan matakin.

Shugaban hadaddiyar kungiyar ma’aikatan kananan hukumomi na kasa, Ibrahim Khalil ya bayyana yadda yunkurin malaman zai shafi ‘yanci kananan hukumomi. Bisa ga cewarsa, tun farko sun zauna sun cimma yarjejeniya da malaman makarantun firamare na kananan hukumomi inda suka bukaci a cire batun albashin malaman daga karkashin kananan hukumomi, amma daga baya, domin neman yin babakere, sai gwamnoni suka kara hankada albashin kananan hukumomin zuwa karkashin gwamnatocin jihohi.

Ga cikakken rahoton da wakiliyarmu Madina Dauda ta aiko mana daga birnin tarayya Abuja.

Zanga zangar malamai 2'45
please wait

No media source currently available

0:00 0:02:45 0:00

  • 16x9 Image

    Grace Alheri Abdu

    Grace Alheri Abdu  babbar Edita ce (Managing Editor) a Sashen Hausa na Muryar Amurka wadda ta shafe sama da shekaru 30 tana aikin jarida. Tana da digiri na biyu a fannin dokoki da huldar diplomasiyar kasa da kasa, da kuma digiri na biyu a fannin nazarin addinan al'adun gargadiya na kasashen Afrika.

Facebook Forum

XS
SM
MD
LG