Rahotanni daga Abuja babban birnin tarayyar Najeriya na cewa, an rufe zauren Majalisar Dokokin kasar, bayan wani harbin bindiga da ya faru a arangamar da ta kaure tsakanin mabiya mazhabar Shi’a da jami’an tsaro.
Wani shaida ya tabbatarwa da kamfanin dillancin labarai na Reuters aukuwar wannan al’amari wanda jaridun Najeriya da dama suka ruwaito.
A yau Talata daruruwan ‘yan Shi’a sun yi zanga zanga a kofar majalisar kasar, suna neman a sako shugabansu Sheikh Ibrahim El Zakzaky da matarsa, wadanda aka tsare tun a shekarar 2015, bayan wani rashin jituwa da ya auku tsakanin mabiyansa da dakarun Najeriya.
Mabiya mazhabar ta Shi’a sun zargi dakarun Najeriya da kashe daruruwan mambobinta a wannan arangama da kuma rushe gidan shugaban na su.
A ‘yan kwanakin nan, rahotanni sun nuna cewa lafiyar El Zakzaky tana tabarbare sanadiyyar rashin lafiya da yake fama da ita da zargin rashin kulawa da ba a ba shi, ko da yake babu wani rahoto da ya tabbatar da hakan.
Arangamar da aka yi tsakanin ‘yan Shi’an da jami’an tsaron a yau, ta kai ga masu zanga zangar sun yi nasarar kwace bindigar hannun daya daga cikin ‘yan sandan da aka girke a kusa da majalisar, lamarin da ya ba su dama suka harbi wasu ‘yan sanda biyu, kamar yadda wasu rahotanni suka nuna.
Wasu bayanai sun yi nuni da cewa masu zanga zangar sun kona motocin da ke yankin majalisar, ko da yake, kamfanin dillancin labarai na Reuters ya ruwaito cewa, babu tabbacin wanda ya yi harbin ko adadin mutanen da suka jikkata sanadiyyar harbin.
A watan Disambar 2016, wata kotun tarayyar a Abuja, ta ba da umurnin a saki Malam El Zakzaky, bayan da lauyoyinsa suka shigar da kara, amma har yanzu hukumomi na tsare da shi.
Rahotanni da dama sun ruwaito hukumomin na Najeriya suna cewa, tsare malam El Zakzaky da suka yi alfanu ne a gare shi, domin a cewarsu suna tsare lafiyarsa ne, hujjar da mabiyansa suka yi watsi da ita.